Bidiyon gabatarwa

SIFAR MAKARANTAR

Makarantar koyon shari'a ta maida hankali ne wajen koyar da ilimin addinin musulunci a hankali, tun daga tushen ilmummukan da musulmi ke bukata, kamar yadda Alkur'ani da Sunnah suka tabbatar. Ta bangaren Aƙida da tauhidi, hadisi, fikihu, tarihi, adabi da kuma harshen larabci, ta hanya mai sauki da ban sha'awa wacce ta dace da waɗanda ba ƙwararru ba a fannin ilimin addinin muslunci, ko wane irin matakin karatunsu, sannan ta daukaka su a matakin ilmin addini musulunci