HANGEN NESA
Tsarin koyarwa na ilimi Wanda zai Kula da koyar da ilimomin shari'ar musulunci ta hanyar yanar gizo ta hanyar kafofi mabanbanta.
Domin cusawa ɗalibai masu koyo wayewa ta musulunci madaidaiciya da Gina kwarewar Kai da Kai garesu, Wanda ya kunsa ababe nagartattun masu biyan buƙata, Kuma su saukake samammiyar fasahar wajen cin ma manufofin da aka tsara.
SAƘON
Makarantarmu tana kokari ne wajen yaɗa ilmin addinin musulunci ta yanar gizo ta hanyar ƙwarewar makarantar ta musmman, da gudanarwa ta ilimi da wayewa ta hanyar buɗaɗɗen manhaji matsakaici, da yanayi na ilmatarwa mai banƙaye, da ingantaccen aikin cibiyoyi da kuma ƙwarewa wajen amfani da fasahar zamani.
BABBAR MANUFA
Cancantar da ɗaliban ilimi bisa kaso Mai tsoka na Neman ilimi da horarwa, tare da kwarewa wajen koyon fannonin shari'ar musulunci ta hanyar manhajin ilimi cikakke Wanda zai hada da sababbun tsare tsare na binciken tarbiyyar ta zamani da Kuma hanyar koyo Wanda zai tabbatar da inganci da wayewa na dukkannin masu koyon