Tambayoyin gama-gari

Ta yaya zan fara karatun

Karatun zai fara da zarar kunyi rijsta a makarantar, kayi rijista yanzu

Tsallaka zuwa shafin diploma

zaɓi diplomar da ka ke so, sannan ka zaɓi kwas ɗin da zaka fara dashi

Saurari bidiyon dake tare da kwas ɗin, kuma kayi bitar darasin

Kayi jarabawa, sannan ka cire shahadarka nan take

Kwasa-kwasan da ke akwai har yanzu kyauta ne, Yi sauri kayi karatun da kyau, sannan jarabawa da kuma samun shahada nan take

Bayan kammala dukkanin kwasa-kwasan diplomar, zaka samu shahadar diploma

Shin akwai wasu sharuɗɗa dn shiga makarantar?

Babu wasu sharuɗɗa, sai di ɗalibi ya kasance ya haura shekara 15,
kuma yayi alƙawalin kallo nazarin abinda ake buƙata sannan yayi jarabawar, kuma duk wanda ya wuce waɗannan shekarun maza ko mata, zamuyi ƙoƙarin yaci gajiyar
wannan makaranta, ba tare da buƙatar wasu takardu na musamman don yin rijista ba.

Ta yaya zan shiga makarantar?

Gme da Shafin Makarantar

Rajistan shigar na nan a saman shafi, sannan kayi rijsta a diplomar da kake so

Ta yaya zan san cewar an karɓeni a makarantar?
Idan kayi rijista a makarantar, sunanka zai bayyana a saman shafin,
kuma shafi na musamman na asusunka da kwasa-kwasanka da
shahadarka zai bayyana a saman shafin.

Shin zan iya yin rijistan diploma fiye ɗaya?
Na'am, zaka iya yin rijistar diploma fiye da ɗaya, Zama ka iya yin
rijistan cikin dukkanin diploma, ta yanda za'a kiyaye cinkaron
lokutansu

Kwas nawa ne a kowane mako, kuma shin akwai cin karo a cikin lokutan?
Yawancin Kwas din sau biyu ne uku a kowane mako,
kuma babu cin karo tsakanin duk lokatan diploma.
Zaka iya yin rajista a dukkan diploma idan kana so.
 

Shin zamu iya sanin suwaye malaman kwasa-kwasan?
Sune manyan malaman ƙasar yaman, da shehunnanta,
da malamanta daga cikin Ahlus-sunna wal-jamaa'ah
waɗanda suke da madaidaicin zance
da kuma ilimi mai tushe.
 

Yaya tsawon lokacin karatu na difloma ɗaya?
Ya bambanta, matsakaiciya na da kwas10, kwatankwacin kwanaki 15,
kuma ranar kusan awa uku ne.”
 

Wace aƙida ce makarantar ta ginu a kanta, kuma wace mazhaba
take bi a fikihu?

Makarantar ta ginu akan manhajin Ahlul-Sunnah Wal-jama’ah,
tare da fahimtar magabata na al’umma, godiya ta tabbata ga Allah.
Amma a diplomar fiƙihu, duk da girmamawarta ga mazhabobinnan
huɗu, ta dauko sharhin Matn Abi Shuja'i, wanda yake cikin mazhabar
Shafi'iyya.

Ina ake watsa kwasa-kwasan? Ta yaya zan iya kallo kuma in shiga
kwas? Shin zai yiwu in shiga kuma in kalli kwas din ko da ba zan iya
kallonsa kai tsaye ba?

A lokacin da aka kayyade na kowane kwas, za ka iya bin kwas ɗin
a cikin shirin Zoom ko kuma ta hanyar watsa shirye-shiryen kai tsaye
a YouTube ko Facebook, kuma duk wanda ya wuceshi saboda dalilin
da ya bijiro zai iya kallon shi a shafin bayan haka ko a YouTube ko
Facebook kuma yana da damar jarabawa.

Shin ina bin hanyoyin sadarwar ku na musamman?
Eh yana da kyau ku bi duk hanyoyin sadarwa da suka shafi tashar,
kuma za ku same su a saman shafin, a cikin su ake aiko da links
da ilimantarwa, kuma a ciki ake yada kwasa-kwasan, muna kira ga
masoyanmu su yi like, share and follow, domin hakan yana daga
aikin alkhairi da kira zuwa ga Allah da karantar da ilimi.

Zaka iya samun Shahadun ka akan shafin ((Kwas dina da Shahadata))

Ina halartar watsa shirye-shiryen kai tsaye, shin zan iya kallo ko

sauraron darasin, sannan in yi jarabawar a kowane lokaci?
Eh, zaka iya kallo ko sauraron duk kwasa-kwasan da aka fara
watsa su kai tsaye, kuma za iya yin jarabawa bayan kayi bitar
manazartar, Idan kaci jarabawar Shahadarka zata bayyana a cikin
"Shahata"
 

Shin ina da damar jarabawa ba tare da kallo ko sauraron kwas ba
ko bitar manazartar?

Duk wanda bai kalla ba, ko bai saurara ba, ko bai karanta
manazartar (littafin) ba, ba zai cancanci jarabawa ba, don haka
kafin jarrabawar ta bayyana, za a ce ya yi alkawarin cewa lallai ya
karanta kwas din.

Bayan kallon darasin sai nayi jarabawa amma ban ci jarabawar ba,

shin ina da damar sake jarabawar?
Ee, kna da damar sake bitar darasin a karo na biyu ta kallo ko
saurare, sannan sake gwadawa.

Me yasa ba zan iya yin jarabawa ba?
Watakila dalili shi ne ba ka yi rajista ba kuma ba ka shiga ba ko kuma ba ka shiga asusunka ba, don haka yi rajista ka yi subscribing yanzu ko kuma idan ka yi rajista a baya kuma ka yi subscribing, to ka shiga za ka ga mahɗar (link) jarabawar kowane Kwas da ka fara.

Daga yaushe ake samun jarabawar kwas? Kuma har zuwa yaushe?
Zai kasance samamme kasa da awa 10 bayan kammala kwas din insha Allahu, kuma zai ci gaba da kasancewa a bude ga duk wanda ya kalli kwas din kuma ya karantata ko da ba a kai tsaye ba.

Shin kallon bidiyon kaɗai ya isa a ci jarrabawar, ko kuma ya zama dole a karanta littafin?
Abinda yafi kyau kuma mafi fa'ida shine a haɗa biyun, idan kuma hakan bai yiwu ba, to muna fatan ɗaya daga cikinsu ya wadatar duk da kasawar.

Ta uaya zamu iya gano amsar daidai?
Ta hanyar komawa ga bidiyo da manazartar(littafin) wanda ke kan shafin kwas ɗin.
Bayan dama ta biyu, manyan tambayoyin zasu bayyana gareka da sanya gyara a gefinsu amma ba tare da bayyanar ingantattun amsoshin ba don gudun ha'inci, kuma zaka iya gano tambayoyin da kayi kuskure a ciki, kuma kayi naziri manazartar da karatunsa da kyau sannan ka sake gwadawa bayan awa biyu.